logo

HAUSA

Ziyarar Xi Jinping ta taimakawa duniya kara fahimtar kasar Sin

2022-11-21 20:11:09 CMG HAUSA

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta shaidawa taron manema labarai Litinin din nan cewa, a kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli karo na 17 na G20 da taron koli APEC karo na 29 tare da kai ziyarar aiki a Thailand. Wannan ziyara ce mai fa’ida kuma ma’anar diflomasiya, wadda ta baiwa duniya damar kara fahimtar kasar Sin.

A cewar Mao, ziyarar Xi Jinping ta wannan karo ta gabatar da shirin kasar Sin ga duniya baki daya, inda ya yi kira ga kasashen duniya, da su kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, da ingiza samun bunkasuwar duniya mai dorewa da yin hakuri da juna da kawo moriya ga daukacin Bil Adama. Xi ya kuma ba da shawarar kafa huldar farfado da tattalin arzikin duniya da hadin gwiwar samar da abinci na kasa da kasa da goyon bayan AU wajen shiga G20, wadanda suka samu karbuwa daga kasashe masu tasowa. (Amina Xu)