logo

HAUSA

Kasashen yammacin Afrika na duba yiwuwar kafa rundunar ko-ta-kwana domin dakile ayyukan ta’addanci a yankin

2022-11-21 11:13:23 CMG Hausa

Kasashen Afrika 7 mambobin shirin Accra ko Accra Initiative, na hadin gwiwar kasashen yammacin Afrika kan tsaro, na duba yuwuwar kafa wata rundunar soji ta ko-ta-kwana, domin dakile ayyukan ta’addanci a yankin.

Ministan tsaron kasar Ghana, Albert Kan Dapaah ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a jiya, domin karin haske kan matakan da aka dauka kawo yanzu, da zummar kare yankunan kasashe mambobin shirin da ma yankin baki daya.

A cewarsa, daya daga cikin muhimman batutuwa da suke mayar da hankali kai shi ne, tabbatar da cewa, babu wani yanki da baya karkashin ikon gwamnati a kasashe mambobin shirin, tare kuma da dakile yunkurin masu ikirarin jihadi na cusawa matasan dake zaune a yankunan iyakoki akidarsu.

A cewar ministan, rashin aikin yi tsakanin matasa wani muhimmin dalili ne na shiga ayyukan ta’addanci. Inda ya ce kokarinsu na shawo kan rashin aikin yi yadda ya kamata ta yadda ba zai zama barazana ga tsaron kasa da yankin ba, jigo ne a shirinsu na dakile ta’addanci a tsakanin kasashe mambobin shirin.

An kaddamar da shirin na Accra ne a watan Satumban 2017, domin karfafa ayyukan tattara bayanan sirri da hadin gwiwa kan tsaro tsakanin kasashe mambobi da suka hada da Ghana da Benin da Cote d’Ivore da Burkina Faso da Mali da Togo da kuma Niger. (Fa’iza Mustapha)