logo

HAUSA

Taron COP27 ya zartas da kafa asusun taimakawa kasashe mafi fama da bala’un sauyin yanayi

2022-11-20 20:18:46 CMG HAUSA

 

Lahadin nan ne, aka kawo karshen babban taron kasashe masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 27 wato COP27 a Sharm el Sheikh na kasar Masar, wanda tun farko aka shirya kammala shi a ranar 18 ga wata, inda mahalartan taron suka zartas da kudurori da yawa, tare da yanke shawarar kafa wani asusu na musamman da za a taimakawa kasashe masu tasowa da wadanda ke fama da matsalar sauyin yanayi.

Taro na wannan karo, ya zartas da kudurori fiye da 10, dangane da yadda za a aiwatar da tsarin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da yarjejeniyar Kyoto da ta Paris da sauransu.(Amina Xu)