logo

HAUSA

An bude kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC

2022-11-18 11:42:48 CMG Hausa

A yau Juma’a ne shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific ko APEC, suka fara gudanar da taron su na shekara, inda ake fatan tattauna batutuwan da suka shafi samar da daidaito, da hade dukkanin sassa da wanzar da ci gaba a dukkanin yankin da ma sauran bangarorin duniya.

Wannan ne karon farko da shugabannin APEC din za su gana ido da ido, tun bayan taron su na shekarar 2018, taron ya kuma zo a gabar da duniya ke fuskantar manyan kalubale da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki, da karuwar zaman dar-dar a sassan duniya, da matsalar sauyin yanayi, da tsawaitar bazuwar annobar COVID-19.

Taken taron na bana shi ne “Bude kofa, da Dunkulewa da cimma Daidaito”, kuma firaministan Thailand Prayut Chan-o-cha ne ke jagorancin sa.  (Saminu Alhassan)