logo

HAUSA

Bangarori a Indonesiya sun yaba da nasarar kammala aikin gwajin layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Jakarta-Bandung

2022-11-18 11:47:34 CMG Hausa

A ranar Larabar da ta gabata ne, wata motar duba layin dogo ta gudanar da cikakken bincike kan layin da ke tsakanin tashar Dekarur? Tegalluar da ta Casting Yard mai lamba 4 na babban titin jirgin kasa tsakanin Jakarta-Bandung, kuma sakamako ya yi kyau. Wannan ya nuna cewa, an samu cikakken nasara a gwajin farko na layin dogo mai sauri tsakanin Jakarta-Bandung da kasashen Sin da Indonesia suka gina cikin hadin gwiwa.

Gwamnan Lardin Java ta Yamma Ridwan Kamil, ya bayyana cewa, wannan shi ne karon farko da daukacin al'ummar Indonesia suka shaida aikin jirgin kasa mai sauri da aka dade ana jira, wanda kuma ke da matukar muhimmanci a tarihi.    

Shugaban Kamfanin hadin gwiwar layin dogo na Sin-Indonesia (KCIC) Dwiyana Slamet Riyadi, ya bayyana cewa, babban titin dogo tsakanin Jakarta-Bandung shi ne layin dogo mai saurin tafiya na farko a yankin kudu maso gabashin Asiya, kuma Indonesia ta koyi abubuwa da dama, kama daga gini zuwa aiki, har ma da kiyaye titin.

Layin dogo da ya tashi daga Jakarta zuwa Bandung shi ne layin dogo mai saurin tafiya na farko a Indonesia da ma yakin kudu maso gabashin Asiya, wanda ya hada Jakarta, babban birnin Indonesia da Bandung, birnin da ya yi fice a fannin yawon bude ido, kuma tsawonsa ya kai kilomita 142. An fara aikin gina layin dogon ne a watan Yunin shekarar 2018. Wannan wani muhimmin aiki ne karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya” da kuma hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Indonesia da ake iya gani a zahiri.(Safiyah Ma)