logo

HAUSA

’Yan sama jannatin Shenzhou-14 sun yi tattaki a sasarin samaniya karo na uku

2022-11-17 15:29:13 CMG Hausa

Hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta bayyana cewa, ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 dake aiki a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin Tiangong, suna gudanar da tattaki a wajen tashar karo na uku.

Bayanai na cewa, za su yi aiki tare don gudanar da tattaki mai yawa, ciki har da shigar da kayayyakin aiki da za a hada tashar.

Wannan shi ne tattaki a sararin samaniya na bakwai, da ’yan sama jannatin za su gudanar a tashar. Ana kuma sa ran zai dauki sa’o’i 6.5. (Ibrahim)