logo

HAUSA

Layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Jakarta-Bandung alama ce ta shiga muhimmin lokacin raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” tsakanin Sin da Indonesia

2022-11-17 20:53:07 CMG Hausa

Duk da tarin ayyukan dake gaban shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Indonesia, ya samu kallon aikin gwajin layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Jakarta-Bandung ta kafar bidiyo tare da shugaban kasar, Joko Widodo. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, layin dogon wani muhimmin aiki ne da aka gudanar karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da shugabannin Sin da Indonesia suka kira, wanda ya zama alamar shiga muhimmin lokacin raya shawarar ta “Ziri Daya da Hanya Daya”, wanda kuma ke da babbar ma’ana. (Zainab)