logo

HAUSA

Peng Liyuan ta gana da uwar gidan shugaban Indonesia

2022-11-17 09:55:46 CMG Hausa

Da yammacin jiya Laraba ne uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping Peng Liyuan ta gana da takwararta ta kasar Indonesia Iriana a tsibirin Bali na kasar.

Daga baya sun kalli nune-nunen kayayyakin fasaha na al’adun gargajiyar Indonesia, inda madam Peng ta jinjinawa Iriana kaunarta kan aikin kiyaye moriyar jama’a, daga bisani ta yi bayani kan matakan da kasar Sin ta dauka da sakamakon da ta samu wajen kandagarki da jinyar cutar Aids. Ta kuma yi fatan kasashen biyu wato Sin da Indonesiya, za su kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu a wannan fannin, ta yadda hakan zai amfanawa al’ummun kasashen biyu. (Jamila)