logo

HAUSA

Masanan kasa da kasa: Jawabin Xi ya nuna dabarun Sin ga ci gaban duniya

2022-11-17 15:15:27 CMG Hausa

Masana da dama wadanda suka hada da tsohon karamin jakadan kasar Amurka dake kasar Sin da jami’in dake kula da kafofin watsa labarai na kasar Rasha da masanin kasar Senegal da jami’in dake kula da kamfanonin kasar Jamus da sauran jama’a sun bayyana cewa, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron kolin G20, ya nuna dabarun kasar Sin wajen ingiza ci gaban duniya.

Dukkansu suna ganin cewa, a cikin jawabinsa, shugaba Xi ya yi tsokaci cewa, ya dace a sa kaimi kan raya duniya mai hakuri da juna da sanin ya kamata, wannan ya nuna dabarun kasar Sin wajen warware matsalar ci gaban duniya da ingiza bunkasuwar kasa da kasa tare. (Jamila)