logo

HAUSA

An kammala aikin gwajin layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Jakarta-Bandung cikin nasara

2022-11-17 10:16:09 CMG Hausa

Aikin gwajin layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Jakarta-Bangund (HSR) dake kasar Indonesia, ya gudana cikin nasara, bayan da wani jirgin kasa ya kammala tafiyarsa a bangaren layin gwajin titin, daga tashar Tegalluar zuwa ta Casting Yard mai lamba 4 jiya Laraba.

An tsara tare da kera layin dogo mai saurin tafiya ne a kasar Sin, inda za a iya gudun kilomita 385 a cikin sa’a guda.

Layin dogon, wani muhimmin aiki da aka gudanar karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, ya hada Jakarta, babban birnin Indonesia da birnin Bandung dake zama birni na hudu mafi girma a kasar, kana babban birnin lardin Yammacin Java.

Titin da aka gina bisa fasahar kasar Sin, da za a iya gudun kilomita 350 cikin sa’a guda, zai kuma rage tsawon tafiya tsakanin Jakarta da Bandung daga kusan sama da sa’o’i uku da ake yi a baya zuwa kimanin mintuna 40 kacal. (Ibrahim Yaya)