logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya bayyana matsayin Sin kan batun Ukraine

2022-11-17 14:19:56 CMG Hausa

Jiya Laraba zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana a yayin taron da kwamitin sulhun majalisar ya kira kan batun kasar Ukraine cewa, kasar Sin tana fatan sassan masu ruwa da tsaki, za su samar da sharuda domin sake gudanar da shawarwari kan wannan batu, alal misali magance aukuwar hadarin nukiliya, da kyautata yanayin jin kai, da rage tasirin da rikicin Ukraine ke haifar wa makamashi da samar da abinci da hada-hadar kudi a fadin duniya, ta yadda za a cimma daidaiton sana’o’in samar da kayayyaki da kuma jigilar su tsakanin kasa da kasa. (Jamila)