logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da shugaban Indonesiya Joko Widodo da firaministar Italiya Giogia Meloni

2022-11-17 11:20:06 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Indonesiya Joko Widodo a tsibirin Bali jiya Laraba da dare agogon wurin. Shugabannin kasashen biyu sun cimma matsaya daya game da gina makomar bai daya ta Sin da Indonesiya, sun kuma amince da kafa sabon yanayin hadin gwiwa mai inganci, yayin da kasashen biyu za su taya murnar cika shekaru 10 da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni a badi.

Shugabannin sun kuma gani da idanunsu kan yadda aka sanya hannu a kan shirin karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare daga dukkan fannoni tsakanin shekarar 2022 da ta 2026 da tsarin hadin gwiwa bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da sauran takardun hadin gwiwa da suka shafi fannonin tattalin arziki da cinikayya da tattalin arziki na zamani da koyon sana’o’i da tsirran magunguna da dai sauransu.

Ban da wannan, bangarorin biyu sun fitar da “Sanarwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin da Jamhuriyar Indonesiya”.

Haka kuma a wannan rana, shugaba Xi Jinping ya gana da firaministar Italiya Giogia Meloni a tsibirin Bali na kasar Indonesiya.

Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya bayyana cewa, yana fatan bangarorin biyu za su yi amfani da majalisun gwamnatocin Sin da Italiya da gudanar da tattaunawa a fannoni daban daban, da daga matsayin hadin gwiwarsu domin neman samun sabbin damamakin neman ci gaba cikin hadin gwiwar kasashen biyu. Bangaren Sin yana fatan ci gaba da karfafa mu’ammala da hadin gwiwa a kan dandalin bangarori daban daban kamar G20 tare da bangaren Italiya, ta yadda za a iya yada ra’ayin bangarori daban daban a zahiri, da tinkarar manyan kalubaloli, kamar na tattalin arzikin duniya da da sauransu cikin hadin gwiwa.

A nata bangare Meloni ta bayyana cewa, bangaren Italiya yana fatan ci gaba da inganta mu’ammala da handin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin cinikayya da al’adu da sauransu. Ta ce, kasar Sin babbar kasa ce a duniya, yanzu nahiyar Asiya ke zama wani bangare mai muhimmanci a duniya a kai a kai, don haka, bangaren Italiya yana fatan yin hadin gwiwa da Sin a MDD da G20 da sauransu. (Safiyah Ma)