logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da babban sakataren MDD

2022-11-16 20:21:50 CMG Hausa

A yau da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres a tsibirin Bali dake kasar Indonesia.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin na goyon baya tsarin duniya karkashin jagorancin MDD. Ya ce a halin yanzu, ana fuskantar kalubale da dama yayin da ake kokarin samun bunkasuwa a duniya, wadanda suka haifar da illa ga kasashe masu tasowa, musamman kasashe marasa karfi. Ya kara da cewa, ya kamata a sanya batun samun ci gaba a gaba da kome a cikin ajandar kasa da kasa, da sa kaimi ga kawo moriya da tabbatar da adalci ga kowace kasa da kowane mutum a wannan fanni. Har ila yau, ya ce Sin tana son kara hada gwiwa da MDD don sa kaimi ga samun sakamako kan kiran samun ci gaban duniya da kiran tabbatar da tsaro a duniya.

A nasa bangare, Guterres ya bayyana cewa, MDD na yabawa kasar Sin domin ta tsaya tsayin daka kan ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Kuma kiran samun ci gaban duniya da kasar Sin ta gabatar ya yi daidai da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD. Kana a fannin taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba, Antonio Guterres ya ce Sin ta fi yin kokari tare da samar da gudummawa. Haka kuma, MDD ta na goyon bayan ka’idar Sin daya tak a duniya, yana mai cewa tilas ne a girmama wannan ka’ida. (Zainab)