logo

HAUSA

Taron G20 ya jaddada kudurin hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen tattalin arzikin duniya

2022-11-16 20:07:32 CMG Hausa

 

Taron kolin G20 karo na 17, ya nanata kudurin hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen tattalin arzikin duniya.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a karshen taron na yini biyu, shugbannin kasashe mambobin kungiyar sun ce, hadin gwiwa ya zama wajibi domin farfado da tattalin arzikin duniya, da shawo kan kalubale da gina tubalin raya tattalin arzikin duniya mai karfi bisa daidaito, kuma mai dorewa.

Mambobin kungiyar sun bayyana kudurinsu na mara baya ga kasashe masu tasowa, musammam matalautan kasashe da kasashe masu tasowa da ke kananan tsibirai, yayin da ake tunkarar kalubalen duniya da cimma muradun ci gaba masu dorewa.

Shugabannin sun kara da cewa, za su hada hannu domin ganin duniya baki daya ta farfado cikin juriya da karfi da samun ci gaba mai dorewa da zai samar da guraben ayyukan yi. (Fa’iza Mustapha)