logo

HAUSA

Sin za ta kara raya sana’o’in dake shafar kasuwar sinadarin carbon

2022-11-16 10:31:38 CMG Hausa

A halin da ake ciki yanzu ana gudanar da babban taron wakilan kasashen da suka daddale yarjejeniyar dakile sauyin yanayi ta MDD karo na 27 wato COP27 a takaice a wurin shakatawa na Sharm el Sheikh dake kasar Masar. Shugaban tawagar wakilan shawarwarin sauyin yanayi na kasar Sin kana mataimakin ministan kare muhallin halittu na kasar Sin Zhao Yingmin ya bayyana a jiya yayin da ya halarci aikin da abin ya shafa cewa, kasuwar sinadarin carbon, na daga cikin manyan manufofin kasar Sin a kokarin kaiwa ga kololuwar fitar da sinadarin carbon zuwa shekarar 2030, kana babban tsarin kirkire-kirkire da ake amfani da shi wajen rage fitar da iska mai gurbata muhalli da tsarin kasuwa.

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin za ta nace kan manufar rage fitar da iska mai gurbata muhalli, ta hanyar amfani da kasuwar sinadarin carbon a fadin kasar, za kuma ta kafa kasuwar sinadarin da za ta yi tasiri a fadin duniya a matakai daban daban.

Tsarin kasuwar sinadarin carbon da gudanar da hadin gwiwa a bangaren, muhimman abubuwan da aka daddale a cikin yarjejeniyar Paris, kuma tabbatar da tsarin, zai taimakawa sassan da abin ya shafa, wajen shiga aikin dakile sauyin yanayi, kuma yanzu haka ana tattauna wannan batu a babban taron COP27. (Jamila)