logo

HAUSA

Trump ya sanar da tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2024

2022-11-16 14:00:53 CMG Hausa

A jiya ne, tawagar tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump, ta gabatarwa hukumar zaben kasar takardar neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a shekarar 2024.

Trump ya shaidawa magoya bayansa da suka taro a gidansa dake Mar-a-Lago a jihar Florida jiya Talata cewa, “Domin kara karfi da daukaka Amurka, ina sanar da anniyata ta tsayawa takarar shugabancin Amurka.” (Ibrahim)