logo

HAUSA

An bude taron kolin shugabannin kasashen G20 karo na 17

2022-11-15 11:05:39 CMG Hausa

Da safiyar yau Talata ne aka bude taron kolin shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 karo na 17, taron da ake sa ran zai mayar da hankali ga batutuwan dake jan hankalin duniya, kamar farfado da tattalin arziki, da inganta tsarin kiwon lafiya, da batun sauyin yanayi.

Yayin taron na yini 2, mai taken "farfadowa tare, farfadowa cike da kuzari", ana fatan tattauna karin batutuwa, kamar sauya akala zuwa ga amfani da na’urori masu kwakwalwa, da batun samar da isasshen abinci da makamashi.

Sassan kasa da kasa dai na fatan manyan kasashe masu wadata, za su karfafa tsarin gudanarwa, a fannin manufofin bunkasa manyan sassan tattalin arziki, da ingiza cudanyar sassa daban daban, da kara bude kofa, da tafiya tare da kowa, da hadin gwiwar cimma moriyar bai daya.

Tun a shekarar 1999 ne aka kaddamar da G20, kungiyar da ta zamo muhimmin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa a fannonin raya hada hadar kudade da tattalin arziki. Kungiyar na da kasashe mambobi 19 da kuma kungiyar tarayyar Turai EU. (Saminu Alhassan)