logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Senegal

2022-11-15 20:58:28 CMG Hausa

Yau da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Senegal Macky Sall a tsibirin Bali dake kasar Indonesia.

Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, bisa kokarin bangarorin biyu, an samu babban ci gaba kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Senegal da kuma Afirka. Ya ce Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da kasar Senegal wajen samun bunkasuwa da farfadowa, da goyon bayan juna kan batutuwan dake shafar cikakken ‘yancinsu, da tsaron kasa, da moriyar bunkasuwa. Ya kara da cewa, Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Senegal wajen gina ayyukan more rayuwa kamar hanyoyin mota, da yankin masana’antu, da kuma fadada fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasar Sin.

A nasa bangare, shugaba Sall ya godewa kasar Sin bisa gudummawarta ga Senegal da kuma sauran kasashen Afirka, yana mai cewa ta kasance kasa ta farko da ta goyi bayan shigar da kungiyar AU cikin kungiyar G20. Ya ce kasar Senegal ta gamsu da ci gaban da aka samu kan ayyukan da aka cimma daidaito kansu, a gun taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, kana tana son ci gaba da hada gwiwa bisa tsarin dandalin tattaunawar.

A wannan rana kuma, shugaba Xi ya gana da shugaban kasar Argentina Alberto Fernández, da firaministan kasar Spaniya Pedro Sánchez, da kuma shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Seok-Youl. (Zainab)