logo

HAUSA

Taron kolin G20 na Bali zai mayar da hankali ga rungumar dama da jagorancin duniya zuwa makoma mai kyau

2022-11-14 14:12:19 CMG Hausa



Za a gudanar da taron kolin G20 na shekarar 2022 a tsibirin Bali dake kasar Indonesiya, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan nan. Shugaban Sin Xi Jinping, da Joe Biden na Amurka, da firaministan Indiya Narendra Damodardas Modi, da shugaban Indonesiya Joko Widodo, da sauran shugabannin kasashen duniya za su hallarci taron kolin. Wannan zai kasance ziyarar farko da shugaba Xi Jinping zai gudanar, tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Ya zuwa yanzu, akwai yanayin rashin kwanciyar hankali a harkokin kasa da kasa, yayin da mambobin G20 ke tsakiyar hadurran da ake fuskanta.

Yawan tattalin arzikin mambobin G20 sun kai kashi 80 cikin dari bisa na duniya baki daya, kana yawan darajar cinikayyar mambobin ya kai kashi 75 cikin dari bisa jimillar na duniya. Kaza lika yawan al’ummun kasashe mambobin kungiyar ya kai kaso biyu bisa uku na jimillar al’ummun duniya.

A sa’i daya kuma, akwai rikice-rikice dake bukatar matakan gaggawa tsakanin wasu kasashen, kamar rikicin cinikayyar Sin da Amurka, da sabanin siyasa dake tsakanin Amurka da Turai da kuma Rasha.

Yanzu haka lokaci ne da ya dace al’ummar kasa da kasa mai yawa ta dauki alhakin ci gaba da tsaron duniya. Taron Kolin G20 ya hade shugabannin kasashen duniya wuri guda, domin tattauna manyan harkokin duniya tare, wanda hakan ya samar da wata dama ta inganta tattaunawa da hadin gwiwa mai amfani.  (Safiyah Ma)