logo

HAUSA

Mutane 6 sun rasu sakamakon fashewar bom a Istanbul na Turkiye

2022-11-14 10:31:44 CMG Hausa

Da yammacin jiya Lahadi ne wani bom ya fashe, a wani titi dake kusa da filin Taksim na birnin Istanbul, birni mafi girma a kasar Turkiye, inda mutane a kalla shida suka rasu, kuma wasu 81 suka ji rauni.

Bayan aukuwar lamarin, gwamnatin jihar Istanbul ta sanar da cewa, bom din ya fashe ne da misalin karfe 4 da mintuna 20 na yammacin jiya Lahadi, kuma nan take ‘yan sanda, da masu aikin jinya da yawan gaske sun isa wurin, an kuma riga an kai wadanda suka ji rauni zuwa asibiti domin samun jinya.

Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya gayawa manema labarai cewa, ana binciken lamarin, kuma sakamakon binciken da aka samu ya nuna cewa, kila fashewar bom din na da alaka da ayyukan ta’addanci da aka tsara.

Shi ma mataimakin shugaban kasar Fuat Oktay, ya bayyana a wani wuri dake kusa da inda fashewar bom din ta auku, cewa mai yiwuwa ne maharin ya tsira, kuma ‘yan sandan kasar suna kokarin tabbatar da ainihin al’amarin. (Jamila)