logo

HAUSA

Kamfanin CCECC na Sin zai gina kasuwar zamani a Addis Ababa

2022-11-14 14:22:35 CMG Hausa

Kamfanin gine gine na kasar Sin CCECC, ya sanya hannu kan takardar yarjejeniya da kamfanin DMC na kasar Habasha, wadda karkashinta CCECC zai gina wata sabuwar kasuwar zamani a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha.

Aikin wanda zai lashe dalar Amurka miliyan 200, zai kunshi babban Otal, da rukunin shagunan cinikayya, da dakunan kwana, a yankin tsakiyar birnin Addis Ababa, kuma idan ya kammala, zai samar da damar bunkasa hada-hadar cinikayya ga matafiya, da manyan hukumomin kasa da kasa, da kuma karin masu zuba jari daga kasashen waje.

Babban jami’in kamfanin DMC Dereje Habtamu, ya ce za a kammala aikin ne cikin shekaru 3 da rabi, zai kuma kasance daya daga manyan ayyuka na raya kasa a Habasha mai kunshe da fasahohin gine-gine na zamani.

Dereje Habtamu, ya ce kamfaninsu ya zabi CCECC ya gudanar da wannan aiki ne saboda ingancin ayyukan ci gaban kasa da yake gudanarwa a Habasha, ciki har da layin dogo na zamani da ya hada birnin Addis Ababa zuwa Djibouti.

Yanzu haka kamfanin CCECC na gudanar da ginin cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka a birnin Addis Ababa, aikin da kasar Sin ke tallafawa gudanar da shi.   (Saminu Alhassan)