logo

HAUSA

Firaministan Sin Ya Gana Da Shugabar Asusun IMF

2022-11-13 16:49:42 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugabar asusun ba da lamuni na duniya, Kristalina Georgieva, jiya Asabar a gefen tarukan shugabannin dangane da hadin kan kasashen gabashin Asia.

Li Keqiang, ya ce yayin da ake fuskantar dimbin kalubaloli, ya kamata kasashe su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu da kuma tsara manufofin raya tattalin arziki, domin kaucewa durkushewarsa.

A cewarsa, bisa mummunan tasirin wasu abubuwa da ba a yi tsammani ba, alkaluman tattalin arzikin kasar Sin sun ragu a farkon rubu’i na biyu na bana, yana mai cewa, amma kasarsa ta aiwatar da wasu manufofin daidaita tattalin arzikin a kan lokaci, da kuma wasu matakai na bibiyarsu, kuma bisa wannan kokari, tattalin arzikin ya farfado tare da samun ci gaba a cikin wannan rubu’i.

Har ila yau, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da inganta aiwatar da cikakakkun manufofin daidaita tattalin arziki, ta yadda alkalumansa za su kasance kan mizanin da ya dace da kara kokarin samun kyawawan sakamako a shekarar baki daya.

A nata bangare, Kristalina Georgieva, ta ce Sin ta dauki matakin da ya dace wajen daukar manufofi yayin da ta tunkari annobar COVID-19, tana mai cewa, manufofin da kasar ta dauka a baya-bayan nan, ingantattu ne da suka dace.

Bugu da kari, ta ce asusun IMF yana jin dadin kyakkyawar mu’amalar dake tsakaninsa da Sin, kuma ya shirya karfafa hadin gwiwarsu. (Fa’iza Mustapha)