logo

HAUSA

Nazarce-nazarce Sun Nuna Yadda Aka Samu Karin Kyautatuwar Ra’ayin Al’ummun Kasashen Masu Tasowa Game da Sin

2022-11-13 17:25:47 CMG Hausa

Wasu nazarce-nazarce biyu da jami’ar Cambridge ta Birtaniya ta gudanar, sun nuna cewa, jama’ar kasashe masu tasowa na kara bayyana kyawawan ra’ayoyi game da kasar Sin.

A karshen watan Oktoba, cibiyar nazarin makomar demokradiyya dake jami'ar Cambridge, ta tattara wasu nazarce-nazarce 30 da suka shafi kasashe da yankuna 137, wadanda ke da kaso 97 na al’ummar duniya, inda suka gano cewa, a kasashe masu tasowa da suka hada da na Latin Amurka da Afrika da Asiya, an samu kyautatuwar ra’ayi game da kasar Sin cikin shekaru 2 da suka gabata. Inda a tsakanin al’ummar Nijeriya, karin ya kai kaso 83 a bana, daga kaso 68 a shekarar 2021.

Haka zalika, wata kuri’ar ra’ayin matasa a kasashen Afrika, ta nuna cewa, kaso 76 daga cikinsu, na ganin tasirin Sin a duniya a matsayin mai kyau. Nazarce-nazarcen sun mayar da hankali ne kan hira ta fuska da fuska da aka yi da matasan da shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 24 a kasashen Afrika 15. Kayayyakin Sin masu inganci da arha da jarin kasar kan ababen more rayuwa a nahiyar da samar da guraben ayyukan yi ga al’umma, na daga cikin dalilan da suka sa mutanen suka bayyana kyakkyawan ra’ayin da suke da shi game da kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)