logo

HAUSA

Sojoji sun hallaka babban dan fashin daji a jihar Kaduna

2022-11-12 16:44:15 CMG Hausa

Mahukunta a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, sun tabbatar da kisan wani kasurgumin dan fashin daji mai suna Dogo Maikasuwa, wanda ya jima yana addabar al’ummun yankin kananan hukumomin Chikun da Kajuru.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a jiya Juma’a, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaron al’umma na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya ce dakarun sojin kasar ne suka hallaka Dogo Maikasuwa, wanda wasu ke kira da Dogo Maimillion. Aruwan ya ce Maikasuwa ya yi suna wajen azabtar da mutanen da ya yi garkuwa da su, tare da kashe wasu idan ya raina kudin fansa da aka gabatar masa.

Ko da yake Aruwan bai bayyana hakikanin wurin da aka hallaka dan ta’addan ba, amma ya ce sojoji sun yi wa Maikasuwa kwantan bauna ne a wani daji, dake yankin kananan hukumomin Chikun da Kajuru na jihar ta Kaduna. (Saminu Alhassan)