logo

HAUSA

Kasar Sin tana goyon bayan bukatar kasashe masu tasowa game da kudaden tallafin sauyin yanayi

2022-11-11 11:15:42 CMG Hausa

Manzon musamman na kasar Sin kan harkokin sauyin yanayi Xie Zhenhua, ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan bukatar kasashe masu tasowa, musamman masu rauni, na neman tallafin kudade daga kasashe masu sukuni, kan asarar da suka tafka da ma barnar da tasirin sauyin yanayi suka haifar musu.

Xie, wanda shi ne wakilin musamman na shugaban kasar Sin, ya bayyana haka ne, yayin wani taron manema labarai da aka shirya a yayin taro na 27 na sassan da suka sanya hannun kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD (COP27).

Ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan taimakawa kasashe masu tasowa, ko da yake bai zama tilas ba, ta hanyar kara karfinsu na juriya ta hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Yana mai cewa, kasar Sin ta samar da gudummawar Yuan biliyan 2, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 275.8 ga kasashe masu tasowa, domin magance matsalar sauyin yanayi.

Xie ya bukaci kasashen da suka ci gaba, da su cika alkawuran da suka dauka a yayin taron sauyin yanayi na Copenhagen, shekaru sama da 10 da suka gabata, na samar da kudade har dalar Amurka biliyan 100 a duk shekara ga kasashe masu tasowa.

Wakilin na kasar Sin, ya kuma yi kira ga kasashe masu sukuni, da su aiwatar da yarjejeniyar Paris baki dayanta, maimakon soke ta. Ya kuma gabatar da nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin samar da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba, da rage yawar iskar methane da ake fitarwa, da tsarin cinikin Carbon.(Ibrahim)