logo

HAUSA

Shugaban kasar Gambia ya jaddada amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya

2022-11-11 20:34:43 CMG Hausa

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ya jaddada amincewar gwamnatin sa da manufar kasar Sin daya tak a duniya. Shugaba Barrow wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya ce Gambia na martaba kyakkyawar alakar kasar sa da Sin, kuma yana fatan zurfafa hadin gwiwa da Sin, domin cimma moriyar juna tsakanin sassan biyu.

Barrow wanda ya karbi takardun kama aiki daga sabon jakadan Sin da Gambia Liu Jin, ya taya kasar Sin murnar kammala taron wakilan JKS karo na 20, tare da godewa Sin din, bisa yadda take matukar tallafawa ci gaban Gambia.  (Saminu Alhassan)