logo

HAUSA

Kamfanin CMI na kasar Sin ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar raya kafofin watsa labarai a kasar Saudiya

2022-11-11 11:31:02 CMG Hausa

 

A jiya ne, kamfanin sadarwa na kasar Sin ko China Mobile International (CMI), ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, da nufin ciyar da yanayin kafofin watsa labaran kasar Saudiya na zamani zuwa gaba.

An gudanar da bikin sanya hannun ne a Riyadh, babban birnin kasar Saudiya, tsakanin kamfanin CMI na kasar Sin, da hukumar kula da harkokin watsa labarai ta kasar Saudiya (SBA), da kamfanin sarrafa na’urorin kwamfuta na kasar Saudiya (SCC) da kuma Whale Cloud.

A cewar hukumar watsa labarai ta Saudiya, a karkashin yarjeneniyar, bangarorin za su hada kai, don samar da hanyoyin sadarwa na zamani, ciki har da kafofin yada labarai na zamani da babu kamarsu a duniya, da cibiyar tattara bayanai da hidimomi, wadanda za a ci gajiyarsu a fannoni na watsa labarai a duniya, da samar da hidimomi da suka shafi harkokin watsa labarai dake kan gaba a duniya.

A jawabinsa shugaban hukumar watsa labarai ta Saudiya, Mohammed bin Fahad Al-Harthy, ya bayyana kudirin hukumar, na gina tsarin samar da hidimar yada labarai da babu kamarsa a duniya, da dandalin dake kunshe da abubuwan da suka shafi harkokin watsa labarai, da yadda za a ci gajiyar kyawawan ayyuka a masana’antar yada labarai dake kan gaba a duniya, don samar da hidimomi na bayanai na zamani da babu kamar su a duniya.

A nasa bangare kuwa, manajan kamfanin CMI na kasar Sin mai kula da yankin gabas ta tsakiya Alex Lee, ya bayyana cewa, kamfanin CMI yana ci gaba da kara zuba jarinsa na samar ababan more rayuwa a yankin gabas ta tsakiya

Baya ga ayyukan hidima na kasuwanci masu inganci da ake kira iSolutions da ma sauran hidimomi a wannan fanni, da kamfanin ke samarwa, CMI yana kuma taimakawa kamfanoni sauyawa zuwa ga tsarin sadarwa na zamani, da ma bunkasarsu a duniya.(Ibrahim)