Bikin CIIE na haifar da moriya ga duniya
2022-11-11 11:23:09 CMG Hausa
Akaluman da aka fitar dangane da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin (CIIE) karo na 5 sun nuna cewa, akwai kasashe da yankuna, da kuma kungiyoyin kasa da kasa kimanin 145 da suka halarci bikin. Kana, wasu kamfanoni fiye da 2800 na kasashe da yankuna 127, sun nuna sabbin kayayyaki da fasahohi kusan 438, adadin da ya dara na bikin bara. Ban da wannan kuma, darajar kwantiragin da aka kulla wajen bikin, wadanda za a aiwatar da su cikin shekara mai zuwa, ta kai dalar Amurka biliyan 73.52, jimilar da ta karu da kashi 3.9% bisa ta bikin bara. Wannan sakamako ya shaida muhimmancin bikin CIIE, musamman ma a fannonin karfafa tunanin bude kofa ga kasashen ketare, da samar da kayayyakin da za su amfani al’ummun duniya.
Haka zalika, a yayin bikin CIIE na wannan karo, an samar da rumfuna kyauta ga kamfanonin kasashe marasa karfin tattalin arziki. Wannan ya taimaka wajen baje kolin kyashu din kasar Guinea Bissau, da barguna kirar kasar Afghanistan, da sauransu, wadanda aka nuna su tare da kayayyaki masu fasahohin zamani na kasashe masu sukuni. Hakan ya nuna yadda ake kokarin tabbatar da adalci da daidaito tsakanin al’ummun kasashe daban daban.
Yanzu haka, an riga an kaddamar da aikin sanin kamfanonin da suke sha’awar halarta bikin CIIE na gaba, inda wasu kamfanoni da kungiyoyi kimanin 60 sun riga sun sa hannu don tabbatar da aniyyarsu ta halartar bikin. Ba shakka bikin CIIE zai ci gaba da samar da moriya ga al’ummun duniya a nan gaba. (Bello Wang)