logo

HAUSA

Jami’in Najeriya ya yi kashedi game da labaran karya da ake wallafa a shafin Tiwita

2022-11-11 10:35:26 CMG Hausa

Ministan watsa labarai da al’adu na Najeriya Lai Mohammed ya bayyana cewa, gwamnati na sanya ido kan labarai da bayanan karya game da kasar dake yammacin Afirka da ake wallafawa a shafin tiwita. Yana mai kashedin cewa, gwamnati ba za ta taba barin wani dandali na sada zamunta ya jefa kasar cikin tashin hankali ba.

Da ya jawabi yayin wani taron manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, Mohammed ya ce, gwamnati ba ta da wani shirin na haramta amfani da wani dandalin sada zamunta ko hana mutane fadin albarkacin bakinsu ba, amma ya yi kashedin cewa, a baya-bayan nan ana yawan samun labarai da bayanan karya game da Najeriya.

Wannan ne ma a cewarsa, ya sa gwamnati ta dakatar da ayyukan Tiwita a kasar a watan Yunin shekarar 2021, bisa zargin dandalin da ba da dama ga masu neman ta da zaune tsaye a kasar, suna wallafa kalamai da bayanan da ba su dace ba.

Daga bisani, aka dage haramcin a watan Janairun bana, bayan da kamfanin na Tiwita ya amince kan wasu sharudda da suka hada da daidaita ayyukansu dangane da labarai da bayanan da ake wallafawa, da biyan dukkan harajin da ya kamata, da kafa reshensa a kasar bisa doka. (Ibrahim Yaya)