logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin zai halarci taron kolin G20 da na APEC

2022-11-11 16:22:22 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta sanar a yau Juma’a cewa, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Indonesiya Joko Widodo ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai tafi tsibirin Bali na kasar Indonesia, don halartar taron kolin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 karo na 17, wanda zai gudana daga ranar 14 zuwa 17 ga watan da muke ciki.

Haka kuma, bisa gayyatar da firaministan kasar Tailand Prayuth Chan-ocha ya yi, shugaba Xi zai je birnin Bankok na kasar, tsakanin ranar 17 zuwa 19 ga wata, don halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin kan kasashen Asiya da yankin tekun Pasific a fannin tattalin arziki (APEC) karo na 29, da zai gudana a kasar Thailand, gami da ziyarar aiki a kasar. Ana sa ran shugaba Xi zai gana da takwarorinsa na wasu kasashe yayin ziyararsa ta wannan karo, wadanda suka hada da Emmanuel Macron, shugaban kasar Faransa, da shugaba Joe Biden na kasar Amurka, da Macky Sall, na kasar Senegal, da dai sauransu. (Bello Wang)