logo

HAUSA

Sanar da Taiwan ganawa tsakanin shugabannin Sin da Amurka da Amurka za ta yi, yana tattare da mummunar manufa

2022-11-11 21:32:32 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce, nufin Amurka na sanar da Taiwan game da ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka za su yi, mataki ne da ya sabawa manufar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyin nan uku, da Sin da Amurka suka amince da su bisa hadin gwiwa, kuma ya nuna mummunan halinta.

Kakakin ya bayyana haka ne, a yayin taron manema labaru da aka saba yi na yau Juma’a 11 ga wata, inda ya jaddada cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta manufar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwoyin nan uku da Sin da Amurka suka amince da su bisa hadin gwiwa, kana ta dakatar da mu'amala a hukumance, da huldar soji tsakanin ta da Taiwan, da kuma dakatar da sayar da makamai ga Taiwan, ta kuma dauki hakikanin matakai don aiwatar da alkawarin cewa, ba za ta goyi bayan "'yancin kan Taiwan" ba, kuma ba za ta jefa alakar Sin da Amurka cikin wani yanayi mai hadari ba.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)