logo

HAUSA

Amurkawa sun kada kuri’a a zaben tsakiyar zango

2022-11-10 11:02:29 CMG Hausa

 

Amurkawa a fadin kasar, sun kada kuri’a a zaben tsakiyar zango mai zafi da aka yi Talata, yayin da ake fuskantar bangaranci da rarrabuwar kawuna.

Zaben ya zo ne a lokacin da kasar ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da na makamashi, da kuma damuwar da ake yi game da fadawarta matsalar tattalin arziki. Sauran batutuwa sun hada da ‘yancin zub da ciki da laifuffuka da manufar amfani da bindiga da na kaura da sauransu.

Bisa kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta NBC ta fitar ranar Lahadi, sama da kaso 70 na masu kada kuri’a a kasar, na ganin cewa, kasar ta kaucewa daidaitaciyyar alkibla.

Nazarin ya kuma gano cewa, kaso 81 ba su gamsu ba kwata-kwata ko kuma suna tababa kan yanayin tattalin arzikin kasar.

Shugaba Joe Biden, wanda ba ya cikin takara a zaben, ya wallafa tarin sakonni a shafin Tweeter, inda ya rika karin haske game da nasarorin da yake ganin gwamnatinsa ta samu, yayin da ya yi gargadin yiwuwar jam’iyyar adawa ta Republica ta mayar da hannu agogo baya. (Fa’iza Mustapha)