logo

HAUSA

Dakarun Somalia sun kashe mayakan al-Shabab 97

2022-11-10 11:13:15 CMG Hausa

 

Dakarun gwamnatin kasar Somalia, sun kashe mayakan kungiyar al-Shabab 97, yayin wasu ayyuka 2 da suka gudanar a yankin tsakiyar kasar.

Ma’aikatar yada labarai da raya al’adu da yawon bude ido ta kasar, ta ce dakarun gwamnati bisa taimakon al’umma, sun kashe mayakan al-Shabab 50 a garin El Gorof na yankin Galgaduud, yayin da jami’an hukumar tattara bayanan sirri ta kasar, suka kashe wasu 47 a yankin Basra.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar jiya a Mogadishu, ta ce gwamnati na yabawa al’ummar yankin da ma abokai na kasashen waje, wadanda suka bayar da gudunmuwa ga nasarar ayyukan da kawar da mayakan al-Shabab da suke shirin kai hare-hare wuraren taruwar jama’a.

Kungiyar al-Shabab dake fafutukar hambare gwamnatin kasar, na fuskantar matsi da farmaki daga dakarun gwamnati. Tun cikin shekarar 2011, aka fatattaki mayakan kungiyar daga Mogadishu, amma har yanzu tana iya kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati da otel-otel da dakunan cin abinci da sauran wuraren da jama’a kan taru. (Fa’iza Mustapha)