logo

HAUSA

An sanya hannu kan yarjeniyoyi na sama da dala biliyan 73 yayin baje kolin CIIE na 5

2022-11-10 21:05:33 CRI

Bayan shafe yini 6 ana gudanar da bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 5, wanda kuma ya kammala a Alhamis din nan, sassan da suka halarci bikin sun sanya hannu kan kwarya-kwaryar yarjeniyoyin cinikayyar hajoji da hidimomi, na tsawon shekara guda, wadanda darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 73.52. Wannan adadi ya karu da kaso 3.9 bisa dari, idan an kwatanta da na shekarar bara.

A bana, baje kolin na CIIE ya hallara baki daga kasashe da yankuna da hukumomin kasa da kasa 145, ciki har da manyan kamfanoni 284 cikin kamfanoni mafiya karfi 500 dake sassan duniya, da kuma jagororin kamfanoni daban daban.

A bana, an samar da dandalin musamman da ya samar da dama, ga kamfanonin fasaha da na samar da na’urori 368, ta halartar bikin ta kafar yanar gizo.

Mashirya bikin sun ce, tun daga shekarar 2018 zuwa yanzu, an gudanar da baje kolin CIIE sau 5 cikin nasara, kuma tuni baje kolin ya zamo wani dandali na bunkasa sabon salon samar da ci gaba da bude kofa, da yayata cudanyar sassa daban daban. (Saminu Alhassan)