logo

HAUSA

An shirya taro tsakanin jam'iyyun siyasa na Sin da kasashen Larabawa

2022-11-09 12:29:15 CMG Hausa

Ofishin hulda da bangarorin ketare na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya kira taro na 3 kan musayar ra’ayi tsakanin jam'iyyun siyasa na Sin da kasashen Larabawa, a jiya Talata. Jami'an da suka halarci taron sun hada da manyan kusoshi na jam'iyyar FLN ta kasar Aljeriya, da jam’iyyar GPC ta kasar Yemen, da dai sauransu.

A yayin taron, Liu Jianchao, darektan ofishin hulda da bangarorin ketare na JKS, ya ce babban magatakardan JKS Mista Xi Jinping da takwarorinsa na kasashen Larabawa, sun gabatar da shawarwari tare, kan yadda za a kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin Sin da kasashen Larabawa, wadda ta nuna yadda za a raya huldar dake tsakanin bangarorin 2 a nan gaba.

Liu ya ce, JKS na son kara yin mu'ammala tare da jami'yyun siyasa na kasashen Larabawa a fannin dabarun gudanar da mulki, da zurfafa hadin gwiwar kasashen ta fuskar aiwatar da shirin “Ziri Daya da Hanya Daya”. Ban da haka, jami'in ya yi bayani kan sakamakon taron wakilan JKS na 20 da aka kammala a kwanakin baya.

A nasu bangare, manyan kusoshin jam'iyyun siyasa na kasashen Larabawa sun taya JKS murnar gudanar da taron wakilanta karo na 20 cikin nasara, gami da bayyana fatansu na karfafa mu'ammala da hadin kai tare da JKS. Sun kuma bayyana cewa, kasashen Larabawa suna son hada kai tare da kasar Sin, don gudanar da taron shugabannin kasashen Larabawa da kasar Sin karo na farko cikin nasara, da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma a duniya. (Bello Wang)