logo

HAUSA

Guterres ya yaba wa kasar Sin kan yadda take kokarin tinkarar sauyin yanayi

2022-11-09 12:25:31 CMG Hausa

A jiya Talata, a gefen taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta MDD karon 27 (COP27) dake gudana a Sharm el Sheikh na kasar Masar, Xie Zhenhua, wakilin musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kana manzon kasar mai kula da batun tinkarar sauyin yanayi, da Zhao Yingmin, jagoran tawagar kasar Sin dake halartar taron COP27, kana mataimakin ministan muhalli na kasar, sun gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres. 

Yayin ganawar tasu, Mista Guterres ya yabawa kasar Sin, kan yadda take kokarin rungumar tsare-tsaren kare muhalli, da daukar hakikanan matakai, musamman ma a fannin raya bangaren makamashi da ake iya sabuntawa. Guterres ya ce, yana fatan tawagar Sin za ta kara yin tasiri a taron COP27, da mu’amala tare da sauran bangarori, don samar da gudunmawa a kokarin tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya.

A nasa bangare, Xie Zhenhua ya ce, kasar Sin na kira ga bangarori daban daban da su cika alkawuran da suka dauka, da aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata. Musamman ma ana fatan ganin kasashe masu sukuni sun gaggauta cika alkawarinsu na ba da tallafin dalar Amurka biliyan 100 ga kasashe marasa karfi a kowace shekara, da gabatar da tsarin rubanya kudin tallafin da ake samarwa, don karfafa amincewar juna da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu sukuni da masu tasowa.

A nashi jawabi, Zhao Yingmin ya nanata muhimmancin da gwamnatin kasar Sin take bayarwa kan aikin tinkarar matsalar sauyin yanayi. Ya ce Sin na son yin aiki tare da gamayyar kasa da kasa, don daidaita wannan matsala yadda ya kamata. (Bello Wang)