logo

HAUSA

AU ta kira taron manyan kwamandojin sojan Habasha da TPLF don aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude da sassa biyu suka cimma

2022-11-08 10:58:22 CMG HAUSA

 

A jiya ne, kungiyar Tarayyar Afirka ko AU a takaice, ta kira wani taron manyan kwamandojin sojan Habasha da na TPLF, bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta din-din-din da aka yi tsakanin sassan biyu.

Kungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, taron da aka kira a Nairobin kasar Kenya, ya yi daidai da sashi na 6 na yarjejeniyar baya-bayan da aka cimma, inda sassan biyu suka amince da shirya taron manyan kwamandojin sojinsu, cikin kwanaki biyar daga lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar, da nufin tattaunawa da tsara fasalin aikin da ake fatan gudanarwa dalla-dalla, da suka hada da kwance damara, bisa la’akari da yanayin tsaro da ake ciki a halin yanzu.

A cewar kungiyar, ya kamata taron ya samar da wata taswirar kai agajin jin kai na gaggawa, da dawo da ayyukan hidima a yankin na Tigray. Sai dai a cewar kungiyar, taron ya ta’allaka ne, kan samar da layin tarho na kota-kwana da bangarorin biyu suka yi cikin sa’o’i 24 bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, domin saukaka sadarwa tsakanin manyan kwamandojojin sassan biyu. (Ibrahim)