logo

HAUSA

António Guterres: Sauyin yanayi na dab da kara ta’azzara a duniya

2022-11-08 20:41:33 CMG Hausa

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bayyana a jiya Litinin cewa, matsalar sauyin yanayi na dab da kara ta’azzara a duniyarmu. Don haka ya zama dole ‘yan Adam su zama tsintsiya madaurinki daya, don tinkarar wannan matsalar da ta riga ta barnata tattalin arziki da huldodin kasa da kasa. In ba haka ba, matsalar za ta kawo karshen bil’adama.

An yi taron koli kan batun yanayi tsakanin wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 27 wato COP27 a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar a jiya Litinin, inda shugabanni gami da kusoshin gwamnatocin kasashe da dama suka halarci taron.

Shugaban kasar Masar, Abdel-Fattah al-Sisi, ya bukaci kasashe masu hannu da shuni, da su cika alkawarin da suka dauka kan batun sauyin yanayi, da taimakawa kasashe masu tasowa, wadanda suka fi jin radadi a jikinsu, sakamakon matsalar sauyin yanayi.

Shugaba Sisi ya ce, ya kamata a kara bada fifiko kan damuwar dukkan kasashe masu tasowa, musamman wadanda ke nahiyar Afirka, da taimaka musu wajen sauke nauyin tinkarar matsalar sauyin yanayi, daidai gwargwadon iyawarsu, gami da yawan kudaden da suka samu. (Murtala Zhang)