logo

HAUSA

WHO ta yi kira da a gaggauta tunkarar matsalar sauyin yanayi

2022-11-08 10:47:50 CMG Hausa

Hans Kluge, daraktan hukumar lafiya ta duniya a nahiyar Turai, ya bayyana yadda ake tunkarar matsalar sauyin yanayi a yanzu, a matsayin wanda baya tafiya yadda ya kamata, baya ga tafiyar hawainiya.

A cewarsa, sauyin yanayi da matsalolin da yake haifarwa, sun zama matsalar lafiya dake bukatar daukin gaggawa. Kuma WHO da abokan huldarta, sun riga sun yi gargadi game da hakan. Yana mai kira ga mahalartar taron sauyin yanayi na MDD na COP27 dake gudana a Masar, da su gaggauta daukar mataki daki-daki, bisa hanyar da ta dace.

Ya kara da cewa, kaucewa fuskantar tsananin zafi da matsanancin yanayi, na bukatar daukar ingantattun matakai, wadanda za su iya tunkarar sauyin yanayi da inganta lafiyar daidaikun mutane da al’umma da ma duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)