logo

HAUSA

MDD ta kebe ranar yaki da cin zarafin kananan yara ta duniya

2022-11-08 10:53:22 CMG HAUSA

 

Babban taron MDD ya amince da wani kudiri da aka gabatar, da nufin ware ranar 18 ga watan Nuwamban kowace shekara, a matsayin ranar yaki da warkewa daga cin zarafin kananan yara ta hanyar lalata da musgunawa da ci da guminsu da ma tashin hankali.

Kudurin na jiya Litinin, ya gayyaci dukkan kasashe mambobin MDD, da kungiyoyin dake cikin tsarin MDD, da ragowar kungiyoyin kasa da kasa, da shugabannin kasashen duniya, da na addinai, da kungiyoyin fararen hula, da sauran masu ruwa da tsaki, da su shirya bukukuwan tunawa da wannan rana ta duniya a kowace shekara, ta hanyar da kowa ke ganin ya fi dacewa.

Haka kuma kudurin, yana karfafa bukatar wayar da kan jama’a game da wadanda cin zarafin yara ta hanyar lalata ya shafa, da bukatar hanawa da kawar da matsalar yin lalata da yara, da cin zarafi da tashin hankali. Sannan wajibi ne, a hukunta masu aikata wadannan laifuka, da tabbatar da zakulo wadanda suka tsira daga wannan ta’asa don yi musu adalci da ma kare su daga sake fadawa cikin wannan bala’i, da ba da damar tattaunawa a fili game da bukatar samar musu da kariya da ma kawar da kyamar da ake nuna musu, da kara samar musu da waraka, da kare musu mutunci da hakkokinsu. (Ibrahim Yaya)