logo

HAUSA

CIIE: Wani kamfanin Sin ya sanya hannu kan kwangiloli da kamfanonin makamashi na kasa da kasa da dama

2022-11-07 11:25:50 CMG Hausa

Rahotanni daga dandalin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasuwannin kasar Sin (CIIE) karo na biyar dake gudana yanzu haka a birnin Shanghai na cewa, rukunin kamfanin bututun jigilar mai na kasar Sin, ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa da kamfanonin makamashi na kasa da kasa da dama, don gudanar da aikin hadin gwiwar ayyukan da suka shafi iskar gas (LNG) da kara bude kofar albarkatun mai da iskar gas na kasar Sin bisa tsari na kasuwa.

Haka kuma kamfanin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da kamfanonin Shell da ExxonMobil, da wasu kamfanonin makamashi na kasa da kasa, don samar da hidimomi, kamar yin amfani da tashoshin mai da iskar gas, da ba da haya da musayar tankuna da suka hade kasashe. Wannan dai shi ne karon farko da kasar Sin ta bude tsarin albarkatunta na bututan jigilar mai da iskar gas ga kamfanonin makamashi na kasa da kasa, ta hanyar bikin baje koli a mataki na kasa.

A jawabinsa, babban manajan sashen kasuwanci na rukunin kamfanin kula da tsarin bututun jigilar mai na kasar Sin Li Tian, ya bayyana cewa, a yayin da ake kara karfafa aikin gina bututun jigilar mai, kasar Sin za ta kara karfin bututan jiligar manta zuwa kasuwannin duniya bisa adalci, da gabatar da wadanda ke shiga kasuwannin kasa da kasa, da janyo hankalinsu wajen bude shafukan yanar gizo, da jerin kayayyaki, da cinikin da suka yi a kasar Sin, da kara bude kofa ga kasashen waje.

A halin yanzu, rukunin kamfanin CNPN, ya sarrafa tare da gudanar da tashoshin jigilar mai da iskar gas guda 7, da karfin jigilar mai sama da tan miliyan 30 a kowace shekara, abin da ya sanya shi zama kamfani mafi girma dake kula da tashoshin jigilar mai a kasar Sin. (Ibrahim Yaya)