logo

HAUSA

An zartas da sanarwar Wuhan a taron COP14

2022-11-07 10:42:24 CMG Hausa

An rufe taron wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniyar Ramsar kan yankuna masu dausayi ko COP14 a takaice a birnin Wuhan dake lardin Hubei na kasar Sin jiya Lahadi, inda aka zartas da sanarwar Wuhan, wadda ta sa kaimi ga bangarorin da su dauki matakai don magance hadarin rasa yankuna masu dausayi a duniya.

Sanarwar Wuhan ta yi nuni da cewa, a cikin shekaru 51 da aka kulla yarjejeniyar Ramsar kan yankuna masu dausayi, duk da cewa, bangarori daban daban sun yi kokarin kare yankuna masu dausayi kamar kare manyan yankuna masu dausayi 2466 a duniya, da biranen dake da irin wadannan yankuna 43, da kuma gabatar da shawarwari guda 19 a wannan fanni, amma fadin yankuna masu dausayi a duniya ya ragu da kashi 35 cikin dari.

Sanarwar ta yi kira da a gaggauta aikin kafa da marbata dokokin da suka shafi fannonin kiyaye da gyara da tafiyar da harkoki da kuma amfani da yankuna masu dausayi yadda ya kamata, yayin da ake kokarin kimanta da kiyaye tsarin yanayin halittun yankuna masu dausayi kamar yadda ake fata.

Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin daji da ciyayi ta kasar Sin Tan Guangming ya bayyana cewa, sanarwar Wuhan muhimmiyar sanarwa ce da bangarori daban daban suka cimma daidaito a kai, wadda kuma ta shaida aniyar duniya a wannan fanni. Sanarwar kuwa ta nuna imani da alhakin Sin wajen kara kiyaye muhallin hallitu da sa kaimi ga aikin kiyaye yankuna masu dausayi. (Zainab)