logo

HAUSA

UNDP: Matsalar sauyin yanayi ta fi cutar sankara muni a wasu yankuna

2022-11-05 16:23:38 CMG Hausa

Wasu sabbin alkaluma da shirin raya kasashe na MDD (UNDP) da dakin bincike kan tasirin sauyin yanayi suka fitar jumma’ar da ta gabata sun bayyana cewa, matsalar sauyin yanayi ka iya ninka cutar sankara ko Cancer muni har sau biyu a wasu sassa na duniya, idan har hayakin carbon mai dumama yanayin duniyarmu ya ci gaba da karuwa.

A cewar binciken, misali Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh, karin mutuwar da ake samu sanadiyar matsalar sauyin yanayi, zai kusa ninka yawan adadin masu kamuwa da cutar sankara a kasar sau biyu, kuma zai ninka har sau goma kan wadanda hadarin mota ke kashewa nan da shekarar 2100.

Sakamakon ayyukan da dan-Adam ke aikatawa, yawan iskar Carbon dioxide da ake shaka yana kai wa wani mataki mai hadarin gaske. Lamarin dake haifar da yanayi na zafi a duniya, da kara yawan zafin yanayi mai tsanani, kamar yadda sabon dandalin dake nazarin sauyin yanayin bil-Adama mai suna Human Horizon Platform ya fitar. Yana mai cewa, idan har ba a dauki managartan matakai ba, hakika matsalar sauyin yanayi, za ta kara tsananta rashin daidaito, da na ci gaba.

Baya ga nazari daga rahotannin ci gaban bil-Adama na shekarar 2020,2021 da kuma 2022, alkaluman sun nuna yadda matsalar sauyin yanayi ke shafar rayuwar jama’a, kama daga mace-mace har zuwa ga yanayin zamantakewa. (Ibrahim)