logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga Amurka da ta dauki matakin da ya dace kan batun zirin Koriya

2022-11-05 16:09:45 CMG Hausa

Zaunanannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana a taron da kwamitin sulhun majalisar ya kira domin tattauna batun dake shafar zirin Koriya jiya da cewa, kasarsa ta bukaci kasar Amurka da ta daina daukar matakin da bai dace ba kan wannan batu, haka kuma ta sauke nauyi dake bisa wuyanta na daukar matakin da ya dace, ta yadda za a sake gudanar da shawarwari mai ma’ana.

Zhang Jun ya kara da cewa, kasar Sin tana mai da hankali kan yanayin da zirin Koriya ke ciki, kuma ta damu kan tsanancewar yanayin, yanzu yanayin kasa da kasa na cikin rudani, don haka tana fatan bangarorin da abin ya shafa, za su yi hakuri da hangen nesa, kada su dauki matakan da ba su dace ba.

A cewarsa, kamata ya yi kwamitin sulhun MDD ya taka rawa ta hanyar yin tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma daidaita matsalar jin kai a kasar Koriya ta Arewa. (Jamila)