logo

HAUSA

Kasar Sin za ta kafa karin yankunan misali 29 na inganta shigo da kayayyaki kasar

2022-11-04 10:24:49 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce za a kafa karin yankunan misali 29 na inganta shigo da kayayyaki kasar.

Hukumomi 8 da suka hada da ta raya kasa da aiwatar da gyare-gyare da ma’aikatar kula da harkokin kudi da babban bankin kasar ne suka yanke shawarar kafa yankunan a wasu larduna da suka hada da Beijing da Shanxi da Xinjiang.

Shugaban sashen kula da cinikayya da kasashen ketare na ma’ikatar, ya ce shirin na fadada shigo da kayayyaki kasar Sin, muhimmin bangare ne na manufar fadada bude kofa. Kuma suna maraba da ’yan kasuwa da masu zuba jari daga fadin duniya, su zurfafa hadin gwiwa da yankunan na misali, da kuma hada hannu wajen saukakawa da aiwatar da cinikayya cikin ’yanci da cin moriyar damarmakin ci gaba da na bude kofa na kasar Sin.

Kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi shigo da kayayyaki daga ketere cikin shekaru 13 a jere. Haka kuma, tana fitar da kayayyaki zuwa kasashe da yankuna 210, baya ga kasancewarta babbar mai fitar da kayayyaki zuwa kasashe da yankuna 60.

A watanni 6 na farkon bana, yawan kayayyakin da suka shigo Sin daga ketare, ya dauki kaso 10.6 na irin wadannan kayayyaki a duniya. Karuwar kayayyakin da ake shigowa da su ya karfafa aikin raya tattalin arziki da samar da ayyukan yi a cikin gidan kasashen dake fitar da kayayyakinsu zuwa Sin. Haka kuma, ya bayar da goyon baya mai karfi wajen samar da kayayyaki a gida da kyautata rayuwar jama’a a kasar Sin. (Fa’iza Msutapha)