logo

HAUSA

Neman kudin tunkarar sauyin yanayi a Afrika zai kasance jigon ajandar taron COP27

2022-11-04 10:12:41 CMG Hausa

Jami’ai a nahiyar Afrika sun ce, neman kudin taimakawa kasashen nahiyar tunkarar matsalolin yanayi, zai kasance jigon ajandar taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayin ta MDD karo na 27 dake karatowa, wanda za a yi daga ranar 6 zuwa 18 ga watan nan na Nuwamba a kasar Masar.

Da suke jawabi yayin kaddamar da rahoton nazari da matakan tunkarar sauyin yanayi a Afrika na 2022 ta kafar bidiyo, jami’an sun bayyana cewa, karbar bakuncin taron, zai ba nahiyar muhimmiyar dama ta neman tallafin kudi da na kwararru da take bukata domin gaggauta komawa amfani da makamashi mai tsafta.

Da yake jawabi, shugaban bankin raya nahiyar Afrika (AfDB) Akinwumi Adesina, ya ce taron ya samar da wata dama na cike gibin kudi dake cikas ga kokarin nahiyar na komawa amfani da makamashi mai tsafta da samun yanayi mai juriya a nan gaba. (Fa’iza Mustapha)