logo

HAUSA

Sin: Ya kamata tawagogin wanzar da zaman lafiya ta MDD su samar da kyakkyawan yanayin jurewa kalubale

2022-11-04 11:18:56 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce kamata ya yi tawagogin MDD masu aikin wanzar da zaman lafiya, su rika samar da kyakkyawan yanayin jurewa kalubale, da ingiza ci gaba a kasashen dake fuskantar tashe tashen hankula.

Geng Shuang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manyan jami’an kwamitin tsaron MDD na jiya Alhamis, ya ce wanzar da ci gaba shi ne kashin bayan samar da zaman lafiya da tsaro. Don haka ya dace sassan kasa da kasa su taimakawa kasashen nahiyar Afirka, da dabarun bunkasa ci gaban tattalin arziki, da inganta yanayin rayuwar al’umma, tare da kafa ginshiki mai karfi na tabbatar da zaman lafiya.

Jami’in ya kara da cewa, karkashin tanadin ayyukan su, da tsare-tsaren ayyukan tabbatar da zaman lafiya, wasu tawagogin wanzar da zaman lafiya sun samar da tallafi ga kasashen da batun ya shafa a fannin bunkasuwa, sun kuma cimma manyan nasarori. Ya ce kamata ya yi MDD ta lura da sakamakon da aka cimma, ta wanzar da nasarorin da aka cimma gwargwadon yanayin da tawagogin ayyukan na ta ke ciki.

Geng Shuang, ya kuma ce Sin ta aiwatar da dimbin ayyuka a Afirka, karkashin asusun wanzar da zaman lafiya da ci gaba na Sin da MDD, ta kuma ba da gudummawar da ta dace, wajen kawar da dalilan aukuwar tashe tashen hankula, tare da karfafa juriyar kasashen da hakan ya shafa, ta yadda suka kai ga samun zaman lafiya mai dorewa.  (Saminu Alhassan)