logo

HAUSA

Yunkurin wasu tsirarun kasashe na bata sunan kasar Sin ta fakewa da kare hakkin bil adama ya sake cin tura

2022-11-02 14:31:37 CMG Hausa

Yunkurin wasu tsirarun kasashe da suka hada da Amurka da Canada, na bata sunan kasar Sin, ta fakewa da ’yancin bil adama ya sake cin tura, yayin da a ranar Litinin, mafi yawan kasashe mambobin MDD suka sake jaddada goyon bayansu ga kasar Sin.

Yayin taron kwamiti na 3 na babban zaman MDD karo na 77, wakilin kasar Cuba ya gabatar da sanarwar hadin gwiwa a madadin kasashe 66 dake mara baya ga kasar Sin, inda a ciki suka jaddada cewa, batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang, da yankin musamman na Hong Kong, da Tibet, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, kana sun bayyana adawar su ga siyasantar da batun kare hakkin bil adama, da amfani da mizani 2, ko tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, ta fakewa da kare hakkin bil adama.

Sanarwar ta nuna cikakken goyon bayan kasashe 6 na yankin Gulf ga kasar Sin, baya ga sauran kasashe kamar Yemen, da Libya, da masarautar Saudiyya, wadanda wakilan su suka yi kira ga dukkanin mambobin MDD da su martaba ikon mulkin kai na sauran kasashe, tare da kauracewa tsoma baki cikin harkokin gidan sauran sassa.

Da yake tsokaci game da hakan, jagoran tawagar kasar Sin a ofishin wakilcin dindindin na MDD Dai Bing, ya ce duk yadda Amurka da sauran tsirarun kasashen yamma, suka yi kokarin fitar da sanarwar hadin gwiwa ta muzgunawa kasar Sin, mummunar manufar su ba za ta boyu ba, kuma tsarin su na cimma nasara zai gamu da cikas.

Dai ya ce manufar wadannan tsirarun kasashe ita ce haifar da rudani game da batun Xinjiang ta yadda za su haifarwa Sin baraka, da dakile ci gaban kasar, da tabbatar da babakeren su, ta fakewa da batun kare hakkin bil adama, suna kuma son ci gaba da yada karairayi game da jihar Xinjiang.  (Saminu Alhassan)