logo

HAUSA

Kwararru daga Afirka za su bukaci cika alkawuran samar da kudaden dakile tasirin sauyin yanayi yayin taron COP27

2022-11-02 10:16:20 CMG Hausa

Kwararru daga nahiyar Afirka za su bukaci kasashen da suka ci gaba, da su cika alkawuran da suka dauka, na samar da isassun kudaden gudanar da ayyukan dakile sauyin yanayi, yayin taron COP27 da zai gudana a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar.

Cikin wata sanarwa da kwararrun karkashin kungiyar raya gabashin Afirka ko IGAD suka fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, sun ce kasashen da suka ci gaba ne ke fitar kaso mafi yawa na iskar Carbon mai dumama yanayi, don haka ya dace su samar da kudaden rage tasirin sauyin yanayi ga kasashe masu tasowa, wadanda ke dandana kuda sakamakon rashin karfinsu na tunkarar wannan kalubale.

Sanarwar ta kara da cewa, a watannin da suka gabata, kasashen Afika da dama sun sha fama da wasu daga cikin munanan tasirin sauyin yanayi, ciki har da ambaliyar ruwa a Najeriya, da fari a yankin kahon Afirka.

Da yake tsokaci game da hakan, daraktan cibiyar hasashen yanayi ta ICPAC dake karkashin kungiyar IGAD Guleid Artan, ya ce nahiyar Afirka na fatan sauran sassan duniya za su fahimci mummunan tasirin da nahiyar ke fama da shi daga sauyin yanayi.

Mr. Artan ya ce tuni kasashe masu wadata suka alkawarta baiwa nahiyar gudummawar dalar Amurka biliyan 100 duk shekara, domin gudanar da ayyukan dakile tasirin sauyin yanayi, amma har yanzu kasashen Afirka ba su gani a kar ba. Daga nan sai ya yi fatan ganin taron na wannan karo, zai yi duba kan alkawuran da aka yi yayin taron COP26 na a birnin Glasgow, ta yadda za a fitar da kyakkyawan tsarin aiwatarwa, wanda kowa zai amince da shi. (Saminu Alhassan)