logo

HAUSA

Jam’iyyar Likud na kan gaba a zaben majalisar dokokin Isra’ila

2022-11-02 11:07:42 CMG Hausa

Alkaluman jin ra'ayin wadanda suka kada kuri'a da kafofin yada labarai na kasar Isra’ila suka fitar a daren jiya Talata, sun shaida cewa, jam’iyyar Likud da ke karkashin jagorancin tsohon firaministan kasar Benjamin Netanyahu, na kan gaba a zaben majalisar dokokin kasar karo na 25 da aka gudanar a wannan rana.

Alkaluman da wasu gidajen talabijin biyu suka fitar sun shaida cewa, magoya bayan Benjamin Netanyahu, da suka hada da jam’iyyar Likud, da ma sauran wasu jam’iyyu uku sun samu kujeru 61 da 62, wanda ke nufin cewa, mai yiwuwa a sake nada Mr. Netanyahu a matsayin firaministan kasar tare da nada ministocin gwamnati.

Majalisa guda daya ake da ita a kasar Isra’ila, wadda ke da kujeru 120, kuma bisa ga doka, jam’iyyar da ta samu sama da rabin kujerun, za ta iya nada ministocin gwamnati. Sai dai sakamakon yawan matsakaita, da kananan jam’iyyu da ke akwai a kasar, babu wata jam’iyyar da ita kadai ta taba nada ministocin gwamnati a tarihin kasar.

Gaba daya jam’iyyu 40, da ma kawancen jam’iyyu sun tsaya takarar zaben da aka gudanar a jiya, kuma ana sa ran bayyana kwarya-kwaryar sakamakon zaben a yau 2 ga wata, kuma za a fitar da sakamakon zabe na karshe a cikin mako guda. (Lubabatu)